Hubbasa zuwa ga Yancin - movie trailer a Hausa harshe

Bidiyo

 

April 22, 2015

 

Sama da shekaru 4,000 da suka wuce, Ubangiji ya bayyana Abraham a Mesopotamia ya kuma ce masa, "Ka fita daga kasarka, da iyalanka, da kuma gidan mahaifinka, zuwa wata kasa da zan nuna maka. Sannan zan daukaka alkaryarka." Abraham ya bi umarnin Ubangiji sai yazo kasar Canaan inda inda ya kasance tare da dansa Isaac da kuma jikansa Jacob, wanda aka sauya sunansa zuwa "Israel".

Israel da yayansa 12 sunyi kaura zuwa Egypt saboda yinwa a kasar Canaan, inda yawansu ya karu zuwa alkarya mai girma. Mutanen Egypt sun razana da karfin alkaryar iyalen Israel da ke zaune tare dasu, dalilin haka sai suka mayar dasu bayi kuma suka saka rayuwarsu cikin kunci da azabtarwa. Bayan shekaru 430 a kasar Egypt, sai Moses ya kubutar dasu daga azabar, suka tsallaka Ruwan Teku zuwa Arabia inda suka karba dokar Ubangiji a Mount Sinai.

Ba a bar Alkarya mutanen Israel da suka fice daga Egypt tare da Moses su shiga kasa mai martababa saboda ba su yi amince da Ubangijiba. An tilasta masu kasancewa masu shawagi na shekaru 40 har sai wata sabuwar alkarya da ta aminta da Ubangiji ta taso sannan su shiga kasa mai martaba tare da Joshua.

A tsawon kusan shekaru 400, Alkalan shari'a ne suka mulka kabilu 12 na Israel kamar yarda hukumcin Moses ya shara'anta. A lokacin da suka so samin sarki kamar kowace kasa, Ubangiji ya zabi Saul ya kasance sarkinsu, wanda ya mulke su na 40, sannan sarki David ya biyo baya wanda ya yi mulkin shekaru 40, da kuma dan David wato Solomon wanda yayi mulki na shekaru 40. A lokacin mulkin Solomon, alkaryar Israel ta kasance mafi daraja, an kuma gina dakin bauta na farko, amma saboda zuciyar Solomon ta fice da Ubangiji sabida tsufa, Ubangiji ya fada masa cewa dansa ba zai mulki kabilu 10 daga cikin kabilunba.

Bayan mutuwar Solomon sai aka raba alkaryar Israe kuma azzaliman sarakuna ne suka mulki kabilu 10 na arewa, wadanda basu da asali da David da Solomon. Alkaryar arewa ta cigaba da anfani da sunan Israel kuma Samaria ta kasance babbar birnin kasar. Karamar Alkarya ta Kudu ta kasance Judah, kuma Jerusalem ne bababan birnin, kuma suna karkashin mulkin kabilar David.

Farawa da sarakuna biyu, mutane 16 daga Alkaryar kudancin sun kasance "Jews" sanadiyar suna alkaryar Judah.

Saboda zalinci Alkarya Arewa ta Israel, Assyrian sun yi masu juyin mulki kima suka kulle su. Sauran Israelawa da suka rage sun kasance masu ma'amala da doeon kasar da aka karba. Za a san wadannan mutane a zaman masu Taimako kuma kabiloli 10 na arewacin Israel ba za ta taba zama alkaryaba.

Za a kama Alkaryar kudu ta Judah zuwa babylon a zaman hukumci don bauta ga wasu abubuwan baut, kuma za a rusa dakin bautar, amma bayan shekaru 70, sai Jews suja dawo Judah, suka sake gina dakin bauta a Jerusalem, suka juma cigaba da kasancewa a karkashin mulkin sarki da ya fito daga zuri'ar David.

A lokacin Almasihu, ana kiran alkaryar Judah a zaman Jadaea kuma tana karkashin mulki Roma. Yesu Almasihu da mabiyansa a gabadaya kasar Judaea, suna rokon gano batattar tinkiyar gidan Israel. Bayan shekaru uku da rabi na wa'zi sai Jews suka ki yarda da Yesu a matsayin mai ceto kuma suka cusa ma gwamnatin Roma ra'ayin ta kashe shi. Bayan kwanaki 3, sai ya tashi da rai kuma ya bayyana ga mabiyansa kafin ya tashi zuwa ga Ubangiji a sama.

Jim kadan kafin a kashe Yesu, yayi wahayi cewa, a zaman hukumci kin amincewa da shi, Jerusalem zata kone, dakin bautar zai rushe, kuma za a kama Jews zuwa kasashe daban-daban. Wannan wahayi ya tabbat a cikin 70 AD a lokacin da sarkin daular Roma Titus ya ci Jerusalem da yaki. Jews sun kasance a watse kasashe daban-daban har tsawon sama da shakaru 1800.

A shekarar 1948, abin mamaki ya faru. An kirkira daular Israel, kuma Jews suka mallaki kasa mai albarka. Kiristoti da yawa na ganin cewa wannan abin al'ajabine da kuma albarka daga Ubangiji, amma shin wannan ne takamaimar albarkar daga Ubangiji, ko kuwa aikin shaidannu ne? Wannan fim din yana da ansa.

 

 

 

mouseover